Uwargidan shugaban kasar Amurka Jill Biden ta ziyarci sojojin Tsaron kasa a wajen harabar ginin Capitol Hill ranar Juma’a, inda ta kai masu kayan kwadayi, ta kuma yi masu godiya saboda kare iyalin ta. Ta ce ɗanta marigayi Beau Biden, yayi aiki tare da Sojojin Kasa na jihar Delaware.