Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Venezuela: Jam'iyyar 'Yan Gurguzu Mai Mulki Ta Sha Kaye a Zaben Majalisa


Shugaban 'yan hamayya da suka suka kayar da jam'iyyar 'yan gurguzu dake mulkin Venezuela

A Venezuela jami'an zaben kasar suka ce 'yan hamayya sun kwace rinjaye a majalisar dokokin kasar, sun yiwa jam'iyyar 'yan gurguzu mai mulkin kasar mummunar kaye.

Hukumomi suka ce duk da cewa akwai wasu gundumomi da ba'a gama kidaya kuri'unsu ba, jam'iyyar 'yan hamayya ta sami kujeru 99 a majalisar dokokin kasar mai wakilai167, yayinda jam'iyyar 'yan gurguzun ta sami kujeru 46. Sakamakon zaben babban koma baya ne ga jam'iyyar 'yan gurguzu wacce ta juma tana mamaye madafun iko na shekaru 16 a kasar.

Jiya Litinin, shugabannin 'yan hamayya sunyi alwashin za su yi amfani da rinjaye da suka samu wajen ganin an saki 'yan hamayyan da gwamnati ta tsare su, amma sun ce ba zasu wargaza shirye shiryen tallafawa jama'a da gwamnati mai ci take aiki da su ba.

Shugaban kasar Venezuela da jar riga wanda jam'iyyarsa ta sha kaye

Venezuela's President Nicolas Maduro arrives at a polling station to vote during congressional elections in Caracas, Venezuela, Sunday, Dec. 6, 2015.
Venezuela's President Nicolas Maduro arrives at a polling station to vote during congressional elections in Caracas, Venezuela, Sunday, Dec. 6, 2015.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG