Shugabar Sashin kare hakkin dan adam na Majalisar DinkinDuniya, Michelle Bachelet ta yi kiran da a tattauna yadda za a kwantar da hankali a Venezuela, kasar da fada rikicn siyasar shugabanci a 'yan kwanakin nan.
"Al'amarin na iya muni ta yadda za a kasa shawo kansa, har ya haifar da mummunan sakamako." Ta ce.
Bachelet ta kuma yi kiran da a gudanar da sahihin bincike kan wasu rahotannin da ke nuna cewa jami'an tsaron Venezuelan sun kashe mutane 20, kuma suka tsare fiye da 350 a zanga zangar wannan makon.
Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi shugaba Nicolas Maduro a ranar Alhamis cewa, "muna nazarin dukkannin zabin da muke da su na abin yi" muddun aka kasa samun hanyar kafa sabuwar gwamnati cikin lumana a wannan kasa ta kudancin Amurka."
Facebook Forum