Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

VOA Ta Kaddamar da Sabon Bidiyo Akan Illar Ta’addancin Boko Haram A Arewa Maso Gabashin Najeriya


Taron kaddamar da bidiyo kan kan illar ta'addancin Boko Haram mai takem "Boko Haram Tattaki Daga Bakar Akida"

Muryar Amurka tare da hadin gwuiwar Cibiyar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Amurka, watau USIP, ta kaddamar da wani sabon bidiyo akan yadda ta’addancin Boko Haram ya shafi arewa maso gabashin Najeriya da kasashen yankin tafkin Chadi

Cibiyar Wanzar Da Zaman Lafiya ta kasa da kasa ta Amurka da Muryar Amurka sun kaddamar da wani sabon bidiyo akan yadda ta’addancin Boko Haram ya nakassa dimbin rayukkan al’ummar Arewa maso gabashin Najeriya.

Sabon bidioyon mai taken “Boko Haram: Tattaki Daga Bakar Akida”, ya nuna yadda rikicin Boko Haram yayi sanadiyarhasarar dubban rayuka, ya kuma raba wasu miliyoyin mutane da gidajensu.

Taron kaddamar da bidiyo kan Boko Haram mai takem Boko Haram Tattaki Daga Bakar Akida da Ibrahim Alfa Ahmed wanda ya taimaka aka hada bidiyon
Taron kaddamar da bidiyo kan Boko Haram mai takem Boko Haram Tattaki Daga Bakar Akida da Ibrahim Alfa Ahmed wanda ya taimaka aka hada bidiyon

Ko wanne irin tasiri wanna bidio yake da shi? Malam Idris, wani mazauninbirnin Washington DC da ya sami halartar kaddamarwar, ya ce idan mutane sun kalleshi daga farko zuwa karshe zasu gane illar barin rikici ya yadu cikin mutane, a maimakon a shawo kansa tun yana dan kankani.

Dangane da irin sako da ake son aikawa al’umma a wannan sabon bidiyon, Ibrahim Alfa Ahmed, daya daga cikin wadanda suka yi ‘dawainiyar hada bidiyon, ya ce sakon da ake son aikawa jama’a shi ne cewa duk da matasalar da mutane arewa maso gabashin Najeriya ke fuskanta, akwai wadanda suka tashi suka yaki ta’addancin ‘yan Boko Haram ta hanyar da suka iya yi

Cikin bakin da aka gayyato har da fitattaciyar mai ‘daukar hotan nan da kuma yin aikin agaji, ‘yar asalin Maiduguri, Fati Abubakar.

Ta ce bidiyon zai nuna rayuwar ‘yan Maiduguri cikin yanayin tashin hankalin da ‘yan Boko Haram suka haddasa.

Ga rahotn Sarfilu Hashim da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG