Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wa Zai Lashe Zaben Shugabancin Amurka ne Yau ? Ga Hasashen 'Yan Duba, Da Wasu.


Bakaken fatar Amurka suna bayyana ra'ayinsu kan zaben shugaban kasa.
Hasashen wanda zai lashe zaben shugaban kasa a Amurka, wani aiki ne mawuyaci. Jam’iyyun siyasa, da kamfanonin dillancin labarai, da masana da masu bincike duk sukan shafe watanni su na nazarin kuri’un neman ra’ayoyin jama’a domin kawai su gano ko wanene zai iya lashe zaben.
Makomar zaben Amurka kan sauran duniya.
Makomar zaben Amurka kan sauran duniya.

Amma duk irin kididdigarsu, gano gaibu abu ne da bai yiwuwa, sai dai sa’a kawai. Amma ga wanda kansa ke yin zafi game da irin wannan kididdiga, akwai wasu hanyoyin hasashen na dabam da wasu keyi a nan Amurka, ba don hakan tabbas ba ne, domin kawai su nishadantar da mutane.

Na farkonsu shi ne wani kanti da ake kira 7-11, wanda a duk lokacin zabe yake fitowa da kofunan shan shayi na manyan ‘yan takarar biyu, domin duk wanda yazo shan shayi ya diba a cikin kofin dan takarar da yake so. Tun shekarar 2000, duk wanda kofinsa ya fi kasuwa a kantin na 7-11, shi ne yake lashe zaben shugaban kasa. A bana, kantin yace jama’a sun yi amfani da irin wannan kofi fiye da miliyan 7, kuma daga ciki, Obama yana da kashi 59, Romney yana da kashi 41.

Sai kuma a fagen wasa, inda ake hasashen cewa idan kungiyar kwallon Redskins ta Washington ta ci wasanta na karshe kafin zaben shugaban kasa, to wanda yake kan kujerar shi ne zai lashe, amma idan aka doke ta, to shugaban dake kan kujera zai fadi, kuma sau 17 cikin 18 ana ganin haka a zabubbukan baya, tun 1937. Watakila idan shugaba Obama yana kula da wannan hasashen, jikinsa zai yi sanyi domin Redskins ta sha kashi a wasanta na ranar lahadi.

Su ma yara kanana wadanda ba su kai shekarun jefa kuri’a ba, sun kada nasu inda Obama ya samu rinjaye. ‘Yan duba masu nazarin taurari sun yi taronsu na bana a New Orleans wadanda suka nada ‘yan duba biyar da suka leka abinda suke lekawa, suka ce Obama zai sake lashe kujerar nan.

Ko ma dai yaya zata kaya, bangarorin biyu sun dukufa wajen yakin neman zabe, da kokarin ganin magoya bayansu sun fito sun jefa kuri’a, domin wannan shi ne dahir!!

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG