Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wahalar Man Fetur Na Ci Gaba Da Tsamari


Wata ma'aikaciyar wani gidan mai a bakin aiki

Wahalar man fetur na daya daga cikin abinda ke kwan gaba kwan baya wajen wahalar samuwa a gidajen man Najeriya.

Man fetur na daya daga cikin ababen da ‘yan Najeriya suka dogara da amfani da shi wajen aiwatar da harkokin yau da kullum. Idan aka ce yayi karanci mutane da dama suna shiga cikin halin kaka naka yi. Wakilin Muryar Amurka Nasiru Yakubu Birnin Yero ya hada mana rahoton musamman inda ya tattauna da masu sana’o’i daban daban da ababen hawa masu amfani da man fetur.

Wata mai hawa motar haya cewa tayi, “A gaskiya an haifar mana da wahala sakamakon wahalar man fetur, ga kudin hawa mota ya kara tsada, inda a da zaka je a naira hamsin yanzu sai ka bada naira saba'in. An kara kudin mai a wajen masu sayarwa amma bamu ji an kara a gidajen mai ba”.

Wani mai sayar da biredi cewa yayi, “Yanzu gashi sai dai mu yi ta cin biredin don kar ya lalace saboda ba ciniki, saboda sai da mai ake sayen kayanmu”. Har da mai abincin sayarwa ma cewa tayi abin ba a cewa komai don da yanzu akwai masu hada hada irin wacce ake yi in ba wahalar mai da yanzu ta dora sanwar abinci karo na biyu”.

Shima wani direban motar da ba ta haya ba yace, a gaskiya muna cikin wani hali. Sai a ki sayar mana da mai a je ana sayarwa ‘yan bumburutu su kuma suna sayar mana naira dari takwas ko dari bakwai. Yanzu haka muna sayen litar mai akan naira dari da goma zuwa dari da sha biyar, a gaskiya bama jin dadi”.

Direbobin motocin haya ma sun koka da cewa suna sayen litar man akan dari da ashirin ne, sannan ga rashin fasinja ga wahalar mai”. Wakilin namu ya tambayi wani manajan gidan sayar da man fetur Haruna Aliyu DK game da wahalar man sai yace masa suma matsalar ta shafesu. Yace, “in dai za a samu man a kuma kawo shi to muma ai zamu sayar da shi”. Wahalar man fetur dai a Najeriya ta dade tana kwan gaba kwan baya ga ‘yan Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG