Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilan Koriya ta Arewa Da Ta Kudu Zasu Gana Akan Wasan Olympic


Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un

Kasashen Koriya biyu na shirin gudanar da taro tsakanin wakilansu ranar 20 ga wannan watan da zai fayyace irin rawar da Koriya ta Arewa za ta taka a wasan Olympic na hunturu da zai gudana a kasar Koriya ta Kudu.

Wakilan kasashen Koriya ta Arewa da ta Kudu sun gana yau Litinin domin tattaunawa akan shirin Arewa na tura ‘yan wasan badujala zuwa wasannin motsa jiki na Olympics na hunturu da za a yi cikin wata mai zuwa a Koriya ta Kudun.

Ana sa ran cewa tattaunawar da za'a yi a kauyen Panmunjom dake kan iyaka zata mayar da hankali kan tsarin rawar da shahararriyar kungiyar badujala ta mata zalla su 16 daga Koriya ta Arewa zata taka a bukin. An ce shugaba Kim Jong Un da kansa ya zabi wadanda ke cikin kungiyar.

Koriya ta Arewa ta ce wakilan da zata tura ‘yan wassanin Olympics na hunturu a Pyeongchang sun hada da mawaka, jami’an gwamnati, ‘yan jarida da ‘yan wasa da dai wasunsu.

Ma’aikatar hadin kai ta Koriya ta Kudu ta ce za a kayyade adadin wakilan da Koriya ta Arewa zata tura a ganawar da zata yi da Kwamitin Wasannin Olympics na kasa da kasa a ranar 20 ga watan Janairu.

Ana daukar matakan sassaucin da Koriya ta Arewa ke dauka dangane da wasannin Olympics din a zaman wani yunkuri na rage zaman tankiya bayan gwaje-gwajen makaman nukiliya da makamai masu linzami da kasar ta yi a shekarar da ta shige.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG