Accessibility links

Wakilinmu Yace Yara Akalla 9 Suka Ji Rauni A Sokoto


Ana raba kayan buda-baki sadaka lokacin azumin Ramadan a masallacin Nasfat dake Utako a Abuja, babban birnin Najeriya.

Wata majiya a asibitin kwararru ta Sokoto ta ce yara uku sun mutu, amma wakilinmu ya ga yara 9 da suka ji rauni a lokacin ture-turen karbar kayan Sallah a gidan gwamnatin Sokoto

Matasa su akalla 9 sun ji rauni su na kwance ana musu jinya a asibitin kwararru na Sokoto, a bayan mummunan ture-turen da ya faru lokacin da daruruwansu suka taru domin karbar kyautar kayan Sallah a gidan gwamnatin jihar ta Sokoto.

Wakilin sashen Hausa, Murtala Faruq Sanyinna, yace ya ga matasa 9 da suka ji rauni a asibitin cikin daren nan, yayin da wata majiya a asibitin ta shaida masa cewa matasa uku sun rasa rayukansu, kuma an ajiywe gawarwakinsu a dakin ajiye gawa na asibitin.

Sai dai kuma wata majiyar dabam ta hukuma mai nasaba da gidan gwamnatin Sokoto, ta ce babu wanda ya rasu a wannan lamarin.

Mazauna unguwar da gidan gwamnatin yake sun ce daruruwan matasa sun taru suka yi cincirindo su na jiran a rarraba musu kyautar kayan Sallah, sun kuma musanta cewa wani turken wutar lantarki ne ya fado ya haddasa gudu da tattake mutane a wurin.

Haka kuma sun ce ba wai rabon kayan buda-baki ne ya tara matasan a wurin kamar yadda aka yi ta fada tun da farko ba.

Har yanzu ba a ji wani labari daga bakin gwamnatin Jihar ta Sokoto kan wannan lamari da ya faru cikin daren nan ba.

Ga cikakken bayanin da Murtala Faruq Sanyinna yayi ma Ibrahim Ka-Almasih Garba a tattaunawarsu kan wannan batun dazu da asuba.

XS
SM
MD
LG