Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgin Kwale-Kwale Ya Kife Da 'Yan Kabilar Rohingya a Rafin Naf


Jirgin Ruwa

Jami'an 'yan sanda a kasare Bangaladesh sunce wani jirgin kwale-kwale dake dauke da mutane 50 yan jindsin Rohingya ya tintsuure a cikin rafin NAF kuma da dama daga cikin su sun halaka.Su dai wadannan mutane suna kan hanyar suneta zuwa makwabciyar kasar Bangaladesh.

‘Yan sanda a kasar Bangaladesh sunce wani jirgin kwale-kwale dake dauke da Musulmai ‘yan kabilar Rohingya har su 50 domin kokarin tsallakawa dasu daga Myanma ajihar Rokhine n zuwa kasar Bangaledesh ya kife a Rafin NAF, kuma mutane biyar daga cikin su ruwa ya wuce dasu 4 daga cikin su yara ne , kana da dama haryanzu ba a gansu ba.

Mahukunta sunce masu aikin ceto sun samu nasarar samo gawar wata mata guda da yara hudu, kana sunce mutane 21 sun tsira

SAma da mutane miliyan daya ne dai yan kabilar ta Rohingya suka tsallaka bakin iyakar

Shiga makwabciyar kasar Bangaladesh a cikin yan kwanakin nan, Tserewar da ‘yan tsirarun al’ummar keyi ya zame dole biyo bayan afka musu da sojojin kasr keyi ne bayan wasu ‘yan taaaddan kabilar ta Rohingya sun kaiwa sojojin kaar hari a wani lokaci.

Wannan ramuwar gayya ya haifar da mummunar bala’I wanda yasha suka daga sassa daban-daban na duniya ciki ko harda jakadar kasar Faransa a MDD Francois Delattre, wanda a satin data gabata neya bayyana wannan ramuwar gayyar amatsayin kokarin kakkabe ‘yan kabilar daga doron kasa dake faruwa a gaban idanun su, sai dai shugabannin kasar ta Myanmar sun soki wannan matsaya na jakadar.

‘Yan kabilar ta Rohingya sun bayyana cewa jami’an sojojin suna kona musukauyukan su dake arewacin jihar Rakhine, kana suna yiwa matar su fyade, tare da kwashe musu kaya da kuma dasa boma-bomai a sassan kauyukan dominkar su koma kauyukan nasu.

Mataimakin Sakataren MDD mai kula da hakkin bil adama Andrew Gilmour yace wannan lamari da ya shafi ‘yankabilar ta Rohingya kusan ace shine irin sa mafi muni a duniya a halin yanzu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG