Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Bindiga Ya Kai Hari a Shagon Sayar Da Bindiga a Amurka


Shagon da aka kai harin bindiga a New Orleans da ke Amurka

Hukumomi a wani yanki da ke wajen birnin New Orleans a jihar Louisiana sun ce wani mutum ya shiga wani shagon da ake sayar da bindiga ya kashe mutum biyu.

Shugaban ‘yan sandan yankin, Sheriff Joseph Lopinto ya ce kwastomomi da ma’aikatan shagon su ma sun budewa dan bindigar wuta a ciki da wajen shagon.

Maharin a cewar kamfanin dillancin labarai na AP ya mutu, sannan wasu mutane biyu sun ji raunuka an kuma kai su asibiti.

Amma sun Samsun sauki.

Harin ya faru ne a yankin Jefferson da ke Metaire da misalin karfe 2:50 na rana.

Shi dai shagon ana sayar da bindigogi ne da harsashai, sannan akwai sashen da ake koyon harbi a cikinsa.

XS
SM
MD
LG