Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Kunar Bakin Wake Ya Tarwatsa Kansa A Jeddah


Yan Sanda Na Binciken Motoci Bayan Da Aka Hari A Jeddah
Yan Sanda Na Binciken Motoci Bayan Da Aka Hari A Jeddah

A yau Litinin, Ministan harkokin cikin gida na kasar Sa’udiyya yace, wani dan kunar bakin wake ya tada kansa da bom a kusa da ofishin Jakadancin Amurka da ke birnin yammaci na Jeddah.

Ma’aikatar tace, jami’an tsaro ne suka tsargu da dan ta’addar, inda suka nufe shi da zummar tuhuma, sai kawai ya tada kansa a wajen.

Inda nan take ya mutu, jami’an tsaro guda 2 kuma suka dan ji rauni aka nufi asibiti da su.

Ofishin jakadancin Amurkan ya fitar da sanarwar cewa, ba wani ma’aikacinsu da ya sami rauni a harin. Sun kuma jaddada gargadin tafiye-tafiye zuwa Sa’udiyya, tare da ba Amurkawa shawarar takaita tafiyen da ba dole bane a cikin kasar.

A shekarar 2004, wasu ‘yan ta’addar da ke da alaka da ta Al-Qaida, suka kaiwa ofishin hari da bama-bamai, inda aka sami musayar harbe-harbe tsakaninsu da jam’ian tsaro Sa’udiyya, har jami’ai guda biyar da ba Amurkawa ba suka mutu a harin.

XS
SM
MD
LG