Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani dan Shekara 25 Ya Kashe Mahaifinsa a Sokoto


Gwamnan Jihar Sokoto Aliyu Magatakarda Wamako
Gwamnan Jihar Sokoto Aliyu Magatakarda Wamako

Wani dan shekara 25 da ake zaton yana ta'ammali da kwaya ya sassare mahaifinsa har Lahira a Sokto

Wani Bello Malami dan shekara 25 da haifuwa ya sare mahaifinsa ya aika shi lahira.

Rahotanni na cewa wanda ake zargin, ya nufaci matar mahaifinsa ne da nufin sararta da adda to hakan bai samu ba sai ya juya kan mahaifinsa dan shekaru hamsin da biyar Malami Aliyu a lokacin da yake salla a daren Lahadi ya sassareshi har ya mutu.

Wani mazaunin anguwar a kofar marke ya kara bayani kan abun da ya faru. Yace abun ya faru ne cikin daren Lahadi. Matar uban tace ta lura mutumin ya shigo da adda lokacin da mahaifin ke salla amma ita sai ta shiga cikin daki. Daga bisani sai ta ji ya fara saran mahaifin nasa da adda. Bayan ta ji shuru sai ta fito amma bata ga mijinta ba. To sai ta nufi makwafta tace ta ga Bello ya shigo da adda yayin da mahaifinsa ke salla amma ta fito bata ga mahaifinsa ba. Sai shi yaron ya fito da adda ya hana kowa shiga cikin gidan.

Lamarin ya sa an shiga bincike inda aka ga jini da sabon tonon kasa wurin da yaron ya binne mahaifinsa. Makwafcin ya kara da cewa yaron yana da alamar hauka domin ya sha zama a Kware inda ake ajiye masu tabin hankali sau da yawa.

Rundunar 'yansandan jihar Sokoto ta tabbatar da aukuwar lamarin kuma tace ta soma bincike a kai kamar yadda kakakin 'yansandan DSP Al-Mustapha Sani ya fada.Yace suna da labarin cewa Bello Malami dan shekara 25 ya kashe mahaifinsa Malami Aliyu dan shekara 55. Yace "Tuni 'yansanda suka dauki gawar mahaifin nasa an kaishi asibiti dan a tabbatar da bincike a kansa shi kuma yaron Bello Malami yana hannu jami'an tsaro dan a tabbatar an yi bincike a kan shi yaron". Kawo yanzu dai babu wani takamaiman bayani amma ana bincike. DSP Al-Mustapha ya kara da cewa "Yaron dan kwaya ne yana cikin maye lokacin da yayi wannan abun"

Kafin bincike ya kankama sai kwaya ta saki yaron, ya dawo cikin hankalinsa. Ana cigaba da bincike.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG