Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani harin kunar bakin wake ya halaka mutane 7 a kwarin Tirah dake can da nisa a wani yankin kasar Pakistan inda 'yan tawaye ke buya.

Wani harin kunar bakin wake ya halaka mutane 7 a kwarin Tirah dake can da nisa a wani yankin kasar Pakistan inda 'yan tawaye ke buya.

Maharin ya fasa boma-bomai a wurin wani taron 'yan tawayen dake tare da gwamnati a yankin Khyber na kabilu a kan iyakar Pakistan da Afghanistan.

Babu kungiyar da ta fitoi ta dauki alhakin kai harin.

Shekaru goma kenan da gwamnatin kasar Pakistan ke fafatawa da kungiyoyin 'yan tawaye masu tsattsauran ra'ayin addini a yankin kasar mai cin gashin kai kadaran-kadahan, tare da taimakon sojojin yankin masu goyon bayan gwamnatin..

XS
SM
MD
LG