Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane 4 Ne Suka Mutu Sakamakon Hadarin Da Wani Jirgin Dakon Kaya Yayi A Abidjan.


Hoton jirgin kenan da yayi hadari a Abidjan na IvoryCoast

Wasu 6 kuma sun jikkata, lokacinda jirgin ya fada cikin teku daf da filin saukar jirgin sama na kasar.

Wani jirgin sama na dakon kaya yayi hadari a Ivory Coast, kuma akalla 'yan kasar Moldova hudu mutu a yau Asabar, lokacinda jirgin yayi hadari cikin teku daf da gabar ruwan kasar, kamar yadda ministan tsaron kasar yayi bayani.

Minista Siddiki Diakite, ya gayawa manema labarai cewa wasu mutane 6 cikin jirgin sun ji rauni, cikinsu harda 'yan kasar Faransa hudu. Majiyoyin tsaro daban daban sun ce mutanen jami'an sojin kasar Faransa ne.

Wata majiyar sojojin Faransa ta gayawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, rundunar sojojin Faransa ce tayi shatar jirgin domin yaki da ta'addanci a yankin Sahel .
Jirgin wanda yake dakaon kayan sojoji, 'Yansanda suka ce akwai mutane 10 cikinsa wanda ya fantsama cikin teku, kusa da babbar tashar jirgin sama dake birni Abidjan, yayinda ake ruwan sama kamar da bakin kwariya.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG