Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgin Fansinjan Kasar Misra Ya Bace A Sararin Samaniya Dauke da Fasinjoji


Irin jirgin Msar da ya bace
Irin jirgin Msar da ya bace

Jirgin da ya bace ya taso ne daga kasar Faransa zuwa kasar ta Misra dauke da fasinjoji 59 da ma'aikata kuma ya bace ne bayan ya shiga kasar ta Misra

Wani labari da dumi-duminsa na cewa wani jirgin saman fasinjan kasar Misra ya bace.

Wata kafa tace jirgin saman mai lambar tafiya MS804 ya taso ne daga birnin Paris kafin tsakan dare akan hanyarsa ta zuwa birnin Alkahira.

Kamfanin jirgin ya sa bayanai a shafinsa na tweeter cewa jim kadan bayan jirgin ya shiga sararin samaniyar kasar Masar, tuntubar juna ta katse tsakaninsu.

Kamfanin jirgin ya tabbatar jirgin yana dauke da fasinjoji hamsin da tara da ma'akatan jirgin su goma.

Idan ba'a manta ba a watan Maris wani mutum dauke da bam din giri yayi fashin wani jirgin saman fasinjan Masar, ya tilastawa jirgin sauka a tsibirin Cyprus

XS
SM
MD
LG