Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Jiragen Ruwa Biyu Sun Yi Karo a Teku Dake Gabashin Ingila.


이탈리아  북부 파르마에서 열린 세계피자경연대회에서 미국 요리사가 반죽을 만들고 있다. 
Laraba masu aikin ceto sun tsamo gawarwaki mutane uku daga cikin teku dake arewacin Ingila, kuma suna neman wasu ma’aikatan jirgin ruwa na dakon kaya su takwas, wadanda jirgin da suke aiki ciki ya nutse dab da gabar ruwan kasar Netherlands, bayanda ya yi karo da wani jirgin ruwa, shi ma na dakon kaya.

A aikin ceton da ake gudanarwa, dogarawan ruwa Dutch sun yi amfani da jirage masu saukar ungulu wajen ceto ma’aikata 13 daga jirgin daukar kayan mai suna Baltic Ace.

Jirgin ruwan wanda yake dauke da tutar kasa r Bahamas yana da ma’aikata 24, ya nutse ne bayan da wani jirgin dakon kaya mai suna Corvus J ya kara masa , a wani bangare na tekun inda ake yawan zirga zirgan jirage, da tazarara kilomita 50 daga tashar jiragen ruwa dake Rotterdam.

Har dai a daren jiyan, jirgin dakon kaya Corvus J, mai dauke da tutar Cyprus yana kan ruwa, kuma babu alamar yana fusknatar hadarin nutsewa.

Har a zuwa daren jiya masu aikin ceto sun gayawa manema labarai cewa suna ci gaba da neman ko watakil a sami wani da rai. Koda yake suka ce bayan sa’ao’I hudu da hadarin zai yi wuya a sami mutum da rai cikin ruwan kankara zai yi wuya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG