Wani mutumin kasar Austireliya da ake yabawa saboda ceton rayuwar jarirai fiye da milyan 2 ta hanyar shafe shekaru yana bada gudunmowar jini ya mutu yana da shekaru 88.
James Harrison wanda jininsa ke dauke da wani nau'in sinadarin protein da ba kasafai ake samunsa ba dake baiwa jiki kariya, ya mutu ne a cikin baccinsa a ranar 17 ga Febrairun daya gabata a wani asibitin Austireliya da ke jihar New South Wales, a cewar kungiyar bada agaji ta Red Cross da ake kira da lifeblood.
Harrison ya ba da gudunmowar jini sau 1, 173, a cikin fiye da shekaru 60 bai taba saba alkawarin daukar jinin da aka yi dashi ba har sa'ar da ya yi ritaya a shekarar 2018 yana da shekaru 81.
A jumlance, an karawa iyaye mata miliyan 2 jinin da ke dauke da kwalaben sinadarin anti-d daga jinin harrison fiye da miliyan 3 a Austireliya tun daga 1967.
A 1999, an bashi babbar lambar girmamawa ta kasar Austireliya da nufin yabawa irin talafawar da yake baiwa lifeblood da kuma shirin hada alluran anti-d.
Dandalin Mu Tattauna