Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Duniya

Wani Samame Ya Yi Sanadin Mutuwar Sojoji 4


Wani sojin kasar Pakistan

Kasar Pakistan ta ce wani samamen da sojoji masu yaki da ta’addanci suka kai a kusa da iyaka da kasar Afghanistan, ya yi sanadin mutuwar akalla sojoji hudu, ciki har da wani babban soja da kuma ‘yan ta’adda bakwai.

Wata sanarwar da rundunar sojin ta fitar, na cewa wannan matakin da aka dauka, ya haifar da musayar wuta mai tsanani, lokacin da dakarun suka zagaye yankin, dake zaman maboyar ‘yan ta’addan.

Haka kuma a arangamar soji daya ya samu rauni, an kuma gano wasu manyan bindigogi da harsasai, har da ababen fashewa.

Yankin na Waziristan an dade da saninsa a matsayin matattarar ‘yan ta’adda, da ke da alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda na gida da waje da ake dora wa laifukan kai hare-hare a Pakistan da kuma kan tawagar sojojin da Amurka ke jagoranta a Afghanistan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG