Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Sanata a Amurka Ya Kamu Da Coronavirus


Sanata Rand Paul

Wani sanata a Amurka, mai suna Rand Paul ya tabbatar cewa ya kamu da cutar ta COVID -19, inda ya zama dan majalisar dattawan Amurka na farko da ya bayyana hakan.

“Gwaji ya nuna cewa Sanata Rand Paul ya kamu da cutar COVID-19. Ya na killace, kuma yana samun sauki," inji wani bayani da aka wallafa a shafin tiwita mallakin wannan dan Republican din mai wakiltar Kentucky.

Sanatan ya fadi cewa jikinsa bai nuna alamomin kamuwa da cutar ba, kuma bai yi wata mu’amala da wani da aka tabbatar ya na dauke da wannan shu'umar cutar ba, an dai gwada shi ne a matsayin, abin da ya kira, "kan-da-garki" ganin yawan tafiye tafiye da kuma kasancewa a hidindimu da ya ke yi.

Tun kwanaki 10 gabanin nan ma'aikatan ofis dinsa su ka fara ayyukan ofis nesa da juna, saboda haka sanatan ya jaddada cewa, babu wani ma'aikacin ofis din da ya yi cudanya da shi bayan kamuwarsa.

Facebook Forum

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni – Dan Kasuwar Gwari A Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG