Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasan Kece Raini Tsakanin Manchester United Da Liverpool


Wata karawar da aka yi tsakanin Liverpool da Everton

Kungiyoyin Manchester United da Liverpool na shirin gwada kaiminsu a ranar Lahadi a ci gaba da gasar Premier League ta Ingila.

Karawar na zuwa ne, kwanaki bayan da Manchester United ta hau saman teburin gasar da maki 36 bayan da ta doke Burnley da ci 1-0 a farkon makon nan mai karewa.

Idan Manchester United ta yi nasarar lashe wannan wasa wanda za a yi a filin was a na Anfield, za ta ba Liverpool tazarar maki shida kenan.

Ita dai Liverpool ita ce ke rike da kofin gasar, amma kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce karawar ta ranar Lahadi, za ta ba kungiyarsa damar auna ko su gwanaye ne a gasar ta Premier League.

Darewa saman teburin gasar ta Premier da Manchester United ta yi, shi ne na farko tun bayan da Sir Alex Ferguson ya daina horar da kungiyar – wato tun a kakar wasa ta 2012-13.

Nasarorin da Manchester ke samu, na zuwa ne bayan da ta buga wasanni 11 a jere ba tare da an doke ta ba tun da aka fara wannan a watan Nuwamba.

Ita dai Liverpool wacce ke rike da kofin gasar, ba ta rasa wasa ko daya a gida ba tun bayan kayen da ta sha a hannun Crystal Palace a watan Afrilun 2017.

Labarai masu alaka

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG