Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Najeriya

Wasu Boma-Bomai Sun Tashi A Barikin Sojoji a Jihar Gombe


Gombe

An sami tashin bama-bamai guda biyu a barikin sojoji dake cikin garin Gombe, daya bom na farko ya tashi wajajen karfe takwas 8 na dare dab da mashigar barinkin, inda sojoji sukayi ta harbe harbe, bayan komi ya lafa sai kuma aka sake samun fashewar na biyu a cikin barikin da misalin karfe goma da rabi 10:30 na dare. Wannan dai ya jefa mazauna unguwar cikin dimuwa da tashin hankali.

Amma sojoji suna gar gadin mazauna anguwar da su zauna cikin gidajensu, kada su fita, sannan wasu yara da suka dawo daga makarantar Islamiyya a cikin barikin sun isa gidajen iyayaensu lafia.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG