Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Bindiga Sun Harbe Dan Takarar Sanata A Jihar Oyo


Wasu da ba'a san ko su wanene ba sun Harbe dan takarar Sanata a tutar jam'iyar ADP, Hon. Temitope Olatoye (Sugar) a Jihar Oyo.

A jiya Asabar ne wasu mutane da kawo iyanzu ba’a san ko su wanene ba suka harbe dan takarar sanata a tutar jam’iyyar African development party, wato ADP, Hon. Temitope Olatoye, da aka fi sani da suna “Sugar”, a kauyen Elesu Lalupon, a cikin karamar hukumar Lagelu.

Temitope Olatoye Sugar shine mai wakiltar mazabar Lagelu da Akinyele daga jihar Oyo, a majalisar wakilan tarayyar Najeriya.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Oyo Mr. Shina Olukolu, ya tabbatar da kisan, yace kawo yanzu basu kama kowa ba, amma suna aiki tukuru don gano wadanda suka aikata wannan aiki.

Kwamishinan ‘yan sandan na jihar Oyo ya cewa basason suyi shaci fadi a halin yanzu, kuma ko akwai wadanda suke zargi ba zasu fadi ba, saboda kada su ranta a na kare, Mr. Shina Olukolu ya kara da cewa jama’a su sani cewa komai dadewa zasu kama wadanda sukayi kisan, kuma yace jama’a suyi hakuri kada suyi wani abu da zai tada zauna tsaye.

Jama’ar garin sun nuna rashin jin dadin su, akan kisan da akayi wa “Sugar”.

Saurari cikakken Rohoton Hassan Umar Tambuwal daga Ibadan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG