Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Jiga-Jigan Jam’iyyar PDP Sun Yabawa Gwamnatin Shugaba Buhari


PDP

A yayin da ‘ya’yan jam’iyar PDP ta adawa a Najeriya ke cigaba da caccakar jam’iyyar APC mai mulki da rashIn shawo kan matsalar tattalin arziki da yawancin yan kasar ke kukan matsanancin hali da suke fuskanta tun hawan gwamnatin shugaba Buhari.

A daya hannun kuma wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP din cewa sukayi halin da Najeriya ta sami kanta a ciki yanzu na daga cikin abinda jam’iyyar PDP bari ne. sun kuma ci gaba da cewa dole ne a yabawa kokarin da shugaba Buhari yake yin a kokarin shawo kan matsalar Boko Haram, da sauran abubuwan ci gaban Najeriya.

Lokacin da yake hira da manema labarai Baraden Bauchi kuma tsohon sakataren shirye shiryen jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Umaru Dahiru, yace “ba haka lamuran yake ba saboda, gwamnatin nan ta zo ta sami aikin zaman lafiya ta fara yinsa, kuma ga aikin tattalin arziki ga kuma aikin gyara rayuwar jama’a musammam yadda za a zauna kasa babu cin hanci da rashawa…”

Shima a nasa albarkacin bakin tsohon dan majalisar Dokokin jihar Bauchi, kuma dan jam’iyyar PDP Abdulmumuni Hassan Ningi, yace suna taya shugaba Buhari addu’a don samun nasarar kudurorin da yasa gaba.

Saurari cikakken rahotan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

XS
SM
MD
LG