Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMURKA: Wasu Kamfanonin Jigilar Jiragen Ruwa Sun Sami Lasisi


Wasu Jiragen Ruwan Jigilar Kaya Wata Tashar Jiragen Ruwa

Gwamnatin shugaba Barack Obama, ta nuna azama, wajen kokarinta na kyautata dangantaka tsakanin ta da kasar Cuba, inda ta maido da safarar jiragen ruwan fasinja dake ke kai-kawo tsakanin kasashen biyu.

Ma’aikatar Baitul Malin Amurka ta baiwa akalla kamfanoni hudu lasisi domin yin jigilar fasinja akan hanyar ruwa mai tsawon kilomita 150, wadanda ke tashi daga kudancin Florida zuwa Havana. Uku daga cikin kamfanonin na yankin Florida ne.

A wani labari makamancin wannan, jirgin saman kamfanin Jet Blue, ya bayyana shirinsa na fara ba da shatar jirage daga birnin New York zuwa Havanan daga watan Yuli mai zuwa.

Harkar jigilar fasinja tsakanin Amurka da Cuba, ba bakon abu ba ne, kafin juyin-juya halin da ‘yan kwamnisanci suka yi a shekarar 1959, wanda shugaban kasar Fidel kasar ya jagoranta, inda suka kifar da gwamnatin Fulgencio Batista mai mulkin kama-karya.

Amurkawa da ke son tafiya zuwa kasar ta Cuba, sukan yi tafiyar ne kan tsauraran matakai, ciki har da tafiye-tafiyen da suka shafi na neman ilimi da yawon shakatawa.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG