Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kusoshin Jam’iyyar APC Basu Halarci Taron Kolinta Ba


Shugabannin jam'iyyar APC mai mulki
Shugabannin jam'iyyar APC mai mulki

Injiniya Buba Galadima da Alhaji Atiku Abubakar na cikin manyan kusoshin jam’iyyar APC da basu halarci taron kolin jam’iyyar ba da aka yi a Abuja

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi taron kolinta ba tare da halartar wasu da ake ganin kusoshinta ne ba.

Daya daga cikinsu, Injiniya Buba Galadima da bai kasance a taron ba, ya yi zargin cewa an hanashi gayyata zuwa taron ne.

Amma sakataren jam’iyyar na kasa Mai Mala Boni ya ce a tasa sanin an gayyaci Buba Galadima zuwa taron.

Haka ma har aka waste daga taron ba’a ga tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ba a taron.

Dr Abubakar Umar Kari ya ce rashin kasancewar Alhaji Atiku Abubakar a taron da walakin, wai goro a miya.

To saidai sakataren jam’iyyar na kasa ya ce rashin kasancewar irinsu Atiku Abubakar a taron bai nuna alamar akwai matsala ba.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG