Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Manoma Sun Rasa Rayukansu a Wani Hadarin Kwalekwale a Jihar Taraba


Hadarin kwale kwale
Hadarin kwale kwale

A cikin karamar hukumar Gassol dake jihar Taraba wasu manoma sun rasa rayukansu sanadiyar hadarin kwalekwale da ya rutsa dasu.

Yanzu haka dai rahotanni daga jihar Taraban sun tabbatar da cewa ana ci gaba da aikin ceto wasu mutane bayan da wani jirgin kwalekwale ɗauke da wasu manoma ya kife, a wani kogi da da akewa lakabi da kwatan Nanido dake karamar hukumar Gassol.

Kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar a yau Litinin mutanen da lamarin ya rutsa da su manoma ne dake kan hanyarsu ta dawowa daga gona. Wani dan yankin ya ce an ceto akalla mutane hudu,yayin da aka samu gawarwaki shida,koda yake kawo yanzu ana cigaba da aikin ceto.

Shima da yake tabbatar da hatsarin kwalekwalen Shugaban karamar hukumar Gassol din Hon.Yahuza Yayau,yace ya zuwa yanzu masu ceto na can na neman sauran wadanda ba’a gano ba.

To sai dai kakakin rundunan yansandan jihar Taraban ,David Misal yace ya zuwa yanzu jami’an yansandan yankin basu bada rahoton abun da ya faru ba,to amma yace zasu cigaba da bincikawa.

Wannan hatsarin jirgin kwalekwalen na ma ko zuwa ne yayin da ake gargadin cewa akwai yuwuwaar samun ambaliya bana batun da yasa shugabanni yin gangamin fadakarwa.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG