Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu sun Yaba da Kiran TY Danjuma na a Kame Masu Neman Tada Zaune Tsaye


Yanzu haka dai kungiyoyi masu zaman kansu na mata da matasa, na yin gangami da kuma yekuwa a kafofin yada labarai wajen gargadin ‘yan siyasa dake yin kamfe game da hatsarin dake tattare da siyasar ko a mutu ko ayi rai.

A daidai lokacin da ya kamata a fara aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da manyan ‘yan takarar shugaban kasa suka rattaba hannu a kai, rahotanni na nuna cewa wasu daga yankin Niger Delta Asari Dokubo da Tomplo sun fito kafofin yada labarai sun ce in har ba a sake zaben shugaba Jonathan ba lallai za a yi yaki a Najeriya.

Alkaluma sun ruwaito cewa wannan batu dai ya tunzura tsohon shugaban rundunar sojan Najeriya Janar TY Danjuma mai ritaya inda har ya fito fili ya kalubalanci fadar shugaban kasa da ta hukunta wadannan mutanen.

Karo na farko kenan da wani babba daga arewacin Najeriya ya fito yana tsawatawa game da munanan kalamai da wasu kan yi. Mainasara Kogo Ibrahim, masani a harkar tsaro, siyasa da huldar kasashen duniya ya yaba da yinkurin da TY yayi.

Kashin farko na kundin tsarin mulkin Najeriya yace Najeriya kasa ce dunkulalla, mai al’ummomi daban-daban tare da kabiloli da yaruka da addinai daban-daban, inda ya ba ko wane bangare hakki na adama dashi kuma a kare mutuncin sa.

Malama Naja’atu Mohammed, mai magana da yawun ofishin kamfe din Janar Mohammadu Buhari, tace anyi ma kundin tsarin mulki karan-tsaye don kuwa an ci amanar kasa kuma ba abinda gwamnati tayi.

Shi kuma Malam Isa Tafida Mafindi mai Magana da yawun Ofishin Kemfe din shugaba Goodluck Jonatahan, cewa yayi arewa bata da wani da za ta yi alfahari da shi kamar shugaba Jonathan.

Yanzu haka dai kungiyoyi masu zaman kansu na mata da matasa, na yin gangami da kuma yekuwa a kafofin yada labarai wajen gargadin ‘yan siyasa dake yin kamfe game da hatsarin dake tattare da siyasar ko a mutu ko ayi rai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG