Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Sun Yi Tsokaci Kan Jawabin Shugaban Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari A Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari na cikin shugabannin kasashen da suka yi jawabi a taron kolin Majalisar Dinkin Duniya yau a birnin New York dake Amurka inda shugaban ya tabo abubuwa da dama.

Bayan da shugaban ya gabatar da jawabinsa wa Majalisar Dinkin Duniya, MDD, akan mahimman abubuwan da suka shafi kasa da kasa da kuma Najeriya 'yan kasar na cigaba da tofa albarkacin bakinsu.

Yayinda wasu suka jinjina masa wasu kuwa gani suke da ya maida hankali akan neman kudaden da aka sace daga kasar kuma aka ajiyesu a kasashen ketare.

Dr. Usman Muhammad mai sharhi akan al'amuran da suka shafi kasa da kasa yana tsokaci akan jawabin shugaban.

Yana mai cewa jawabi ne mai nauyi amma dan kadan. Yana da mahimmanci saboda shugaban ya tabo nahiyar Afirka da ECOWAS da siyasar duniya da rubuce rubuce da batun 'yan gudun hijira da kuma kasashen dake tamaimaka wa 'yan gudun hijiran, musamman na kasar Siriya.

Shugaba Buhari ya bada shawarar yadda za'a fitowa muguwar manufar shugaban kasar Koriya ta Arewa.

Akan cewa bai mayar da hankali akan dawowa Najeriya kudadenta da aka sace ba, Dr Usman yace irin wannan maganar ba 'a yinta a waje dalili ke nan da zai gana da Shugaban Amurka Donald Trump domin tattauna al'amarin.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:29 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG