Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Tsoffin Jami'an Leken Asirin Amurka Sun Caccaki Shugaba Trump


John Brennan tsohon shugaban hukumar CIA
John Brennan tsohon shugaban hukumar CIA

Amincewar da Shugaba Trump yayi cewa ya yadda Shugaba Putin na Rasha bai yiwa zaben Amurka na shekarar 2016 shigshigi ba ya batawa wasu manyan tsoffin jami'an leken asirin kasar rai.

Wasu tsoffin jami’an leken asirin Amurka biyu sun caccaki Shugaba Donald Trump jiya Lahadi, cewa Trump ya yi imanin cewa Shugaban Rasha Vladimir Putin “na jin da shi da kasarsa Rasha ba su yi katsalandan ba” a zaben Shugaban kasar Amurka na 2016.

A wata hira da gidan talabijin na CNN, tsohon shugaban hukumar leken asiri, ( CIA), John Brennan, da tsohon shugaban hukumar leken asiri na tsaron kasa, James Clapper, sun ce alamar tun farko da Trump ya nuna cewa ya yadda da abin da Putin ya ce na nuna cewa, “Shugabannin wasu kasashe na iya yaudarar Trump ta wajen zuga da da kuma amfani abubuwan da ya ke da fargaba a kansu, wanda hakan abu ne mai tayar da hankali ta fuskar tsaron kasa.”

Clapper ya ce Rasha “na matukar barazana ga muradun Amurka, kuma duk wani ra’ayi mai nuna akasin hakan na da hadari ga kasar.”

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG