Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Abkawa 'Yan Canji a Fatakwal, Mutum Hudu Sun Mutu


Wasu 'yan bindiga
Wasu 'yan bindiga

A Fatakwal babban birnin jihar Rivers wasu 'yan bindiga da ba'a tantancesu ba su kashe 'yan canji hudu wadanda 'yan asalin jihar Bauchi ne tare da jikkata mutum daya amma kuma 'yan bindigan basu dauki ko kwandala ba

Rashin tsaro ya sake dawowa a jihar Rivers, musamman a babban birnin jihar, wato Fatakwal inda 'yan bindiga ke ci gaba da cin karensu ba babbaka saboda dare da rana ake bin mutane ana bude masu wuta.

A baya-bayan nan, wasu 'yan bindiga da ba'a tantancesu ba suka je inda masu sana'ar canjin kudaden waje suke aiki, suka bude masu wuta, suka kashe mutane hudu kana suka jikata daya.

Tun lokacin aukuwar wannan lamari, 'yan canjin na zaman zullumi saboda basu san abun da ka iya biyo baya ba.

Har yanzu rundunar 'yan sandan jihar ba ta ce uffan ba dangane da gano wadanda suka aikata ta'asar. Usman Makarfi shugaban kungiyar 'yan canji dake Fatakwal ya bayyana yadda lamarin ya faru.

A cewarsa gaskiya ne wasu 'yan bindiga sun farma 'yan kungiyarsa cikinsu har da mataimakinsa inda suka bude masu wuta.An kashe hudu amma daya ya tsira da ransa. 'Yan bindigan basu dauki kudi ba, lamarin da ya kara daurewa mutane kai.

Wasu ganau sun yiwa Sashen Hausa karin bayani. Rabiu Muazu ya ce lallai suna tsaye sai suka ga mutane uku da bindigogi a hannunsu, suka bude wuta har wani cikinsu na cewa "mun gama dasu". Mutum daya da ya tsira, ya taho a guje yana cewa an "harbe mana 'yanuwa".

Yanzu haka 'yan canjin suna zaman jimame. Tsaron da suke samu ba abun da ya taka kara ya karya ba ne.

Shi ma Abubakar Ahmed yace, 'yan bindigan da suka zo ba su ce komi ba sai suka fara harbi.

Alhaji Musa Saidu, wani shugaban al'umma ya yi tsokaci dangane da matsalar. Ya ce mutanen harin ya rutsa da su 'yan asalin jihar Bauchi ne, kuma a iya saninsa basa gaba da kowa a kasuwancin da suke yi. Amma an kashe hudu a cikinsu ba tare da daukan komi ba. Ya ce mutanen da suka aikata wannan mummunan aikin ba'a san kowane irin mutane ne ba.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Umoni Nnamdi, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce suna kokarin tantance yadda lamarin ya faru da zummar zakulo wadanda suka aikata wannan danyan aikin.

A saurari rahoton Lamido Abubakar Sokoto domin karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG