Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 30 AJihar Binuwai


Gwamnan jihar Binuwai da wasu shugabannin Fulani

'Yan bindiga sun hallaka kimanin mutane talatin a kananan hukumomin Guma da Logo cikin jihar Binuwai a wani hari da suka kai kamar yadda mai ba gwamnan jihar shawara a kan al'amuran labarai ya tabbatar

Mutane kimanin talatin ne 'yan bindiga suka hallaka a kananan hukumomin Guma da Logo dake cikin jihar Binuwai.

Tahab Akejuwa wanda yake ba gwamnan jihar shawara a kan harkokin manema labarai shi ya tabbatar wa Muryar Amurka aukuwar lamarin. A cewarsa an samu gawarwakin mutane ashirin ana neman sauran. Tara daga cikin wadanda aka kashen jami'an dake kiyaye dokar hana kiwon dabbobi a fili ne da gwamnatin jihar ta kafa a shekarar da ta gabata.

Bayanai sun nuna cewa akwai wasu mutanen kimanin 30 da suka jikkata da suka hada da mata da kananan yara.

Ardo Turai ya ce dawo da hulda da sarakunan gargajiya da shugabannin Fulani shi ne mafita wajen samun zaman lafiya a jihar. Ya ce kwamitin da gwamnati ta ba bindiga ba hanyar neman zaman lafiya ba ce. A cewarsa gwamnatin jihar ba ta damu da sarakuna ba, wato sarakunan Tivi da na Fulani. Ya kira gwamnatin tarayya ta nemi hanyar mayar da sarakunan gargajiya domin a samu masalaha.

A jihar Nasarawa, jihar dake makwaftaka da Binuwai, rahotanni sun nuna daruruwan jama'a ne ke kwarara cikin yankunan dake kan iyaka domin neman mafaka.

Peter Ahemba shugaban al'ummar Tivi a jihar Nasarawa ya ce mutane sun gudo daga Binuwai su na karamar hukumar Keana a wata makaranta inda suka samu mafaka. Duk da cewa babu kashe-kashe a kauyukan da suka taso amma tsoro ya sa suka gudu saboda suna ganin mutane suna wucewa da bindigogi suna shiga jihar Binuwai kamar zasu yaki.

Shi kuwa gwamnan Nasarawa Umaru Tanko Almakura ya jawo hankalin mutane ne akan su ci gaba da yin hakuri da juna su zauna tare cikin lumana domin a samu zaman lafiya.

Zainab Babaji na da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG