Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Giya Sun Markade ‘Yan BB Shida a Gombe


Sfeto-Janar na 'Yansandan Najeriya, Abubakar Adamu Mohammed.

Jama'ar birnin Gombe sun ga wani abin tashin hankali bayan da wasu bugaggu da giya, wadanda ake kyautata zaton jami'an tsaro ne ma, su ka markade 6 daga cikin mambobin kungiyar BB da ke macin Easter a birnin Gombe.

A wani al’amari mai tayar da hankali, wasu bugaggu da giya, wadanda ake kyautata zaton jami’an tsaro ne, sun markade wasu ‘yan Boys Brigade (BB), lokacin da su ke macin ranar Easter jiya Lahadi a birnin Gombe, hedikwatar jahar Gombe, inda ya zuwa yanzu shida daga cikin yaran su ka mutu.

Su ma bugaggun jami’an tsaron da su ka markade yaran an kashe su, a cewar wani jami’in kungiyar ta BB wanda ya shaidi al’amarin.

Sakataren Majami’ar ECWA na Jahar Gombe, Rev. Adamu Dauda, wanda ya je asibitin ya gane ma kansa. Ya tabbatar da mutuwar ‘yan BB din guda shida, a yayin da kuma wasu ashirin da shida kuma ke samun jinya saboda raunukan da su ka ji sanadiyyar yin ta kansu da bugaggun jami’an tsaron su ka yi.

Saidai ya zuwa lokacin da aka turo wannan rahoton, jami’an tsaro ko rundunar ‘yan sandan jahar ba ta ce komai kan batun ba.

Ga Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG