Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

John Kerry Ya Gana Da Jami'an Gwamnati Da 'Yan Hamayya A Masar.


Daga hagu ministan harkoin wajen Masar kamel Amr, sai sakataren harkoin wajen Amurka John Kerry, daga dama kuma, shugaba Mohammed Morsi.
Daga hagu ministan harkoin wajen Masar kamel Amr, sai sakataren harkoin wajen Amurka John Kerry, daga dama kuma, shugaba Mohammed Morsi.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya gana da jami’an gwamnatin Masar da kuma wasu ‘yan hamayya a ziyararsa ta farko da ya kai alkahira a mtsayinsa na babban jami’in difilomasiyyar Amurka tun kama aiki.

Wasu manyan ‘yan hamayya a Masar sun ki su gana da Mr. Kerry suna cewa Washingtontana goyon bayan ‘yan kungiyar “yaku musulmi”, ko Muslim Brotherhood, masu mulkin Masar ahalin yanzu a rikicin siyasar da ake yi a kasar.

Mohammed ElBaradei, wanda shine jagoran kungiyar ‘yan hamayya da ake kira NSF, yaki ya gana da babban jami’in difilomasiyyar Amurkan, haka wasu manyan jami’ai a bangaren ‘yan hamayya biyu, Hamdeen Sebahi, da Sayeed al-Badawi. Amma wasu shugabannin ‘yan hamaya kamar su Amr Mousa da Ayman Nour sun yi magana da sakataren harkokin waje Amurkan.

A lokacin wani taro da manema labarai da ministan harkokin wajen Masar Mohammed kamel Amr, Kerry yace ya kai ziyara kasar ne domin goyon baya ga jama’ar Masar, ba domin ya goyi bayan wani banagare a rikicin siyasar da ake yi a kasar ba.
Masu zanga zanga da yawa ne suka hallara a a harabar ma’aikatar harkokin wajen Masar lokacinda Mr. Kerry yake ganawa da ministan harkokin wajen kasar Mr. Amr.
XS
SM
MD
LG