Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Kai Hari A Madagali


Wasu ‘yan mata yan kunar bakin wake suka kai hari a Madagali.

Wasu mata uku ‘yan kunar bakin wake sun tarwasa kansu a shinge da Sojoji da ‘yan banga suka kafa a mashigin kasuwar Madagali dake jihar Adamawa inda suka kashe mutun suka yin sanadiyar mutuwar mutun daya da kuma raunata wasu mutane uku.

Kwamishinan yada labarai na jihar Adamawa Alh. Ahmed Sajoh wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce nasarar da jami’an tsaron suka cimma alama ce ta himmantuwar da gwamnati da jami’an tsaro suka yi na gangamin fadakar da jama’a yadda zasu gano ‘yan kunar bakin wake.

Sai dai rahotanni da ke fitowa daga yankin na sabawa juna na adadin wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka ji raunuka kamar yadda jami’in hulda da jama’a, na rundunar ‘yan sanda, ta jihar Adamawa, SP Othman Abubakar, da kuma shugaban karamar hukumar madagali Mohammed Yusuf suka shaida.

Tawarwasa ‘yan kunar bakin wake na baya-bayan nan shine na uku, a kasa da watanni biyu. Jami’an tsaro suka tarwasa biyu daga cikin ‘yan kunar bakin waken.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

XS
SM
MD
LG