Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanzu haka dai ana nan ana tattara sakamakon zabe, amma ya zuwa lokacin da muka sami wannan rahoton akwai rumfunan da ake cigaba da jefa kuri’a a jihohin Sokoto da Kebbi.

Duk da tsaikon da aka samu da kuma wasu ‘yan matsaloli da aka fuskanta musamman da na’urar tantance katin zabe da ma kamala zabe a makare a wasu rumfuna a jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara, ‘yan siyasa da masu zabe sun bayyana gamsuwarsu da sabon tsarin gudanar da zabe.

Sanata Abdallah Wali dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Sokoto, shi ma ya bayyana gamsuwarsa da sabon tsarin, abinda yace zai magance matsalar magudin zabe dake addabar tsarin zabe a Najeriya.

Ita ma jam’iyyar Adawa ta APC ta jinjinawa hukumar zaben Najeriya akan sabon tsarin. Sani Hukuma Zauro, babban jigo ne a jam’iyyar APC a jihar Kebbi shima ya yabawa shugaban hukumar zabe Alhaji Attahiru Jega saboda sabon tsarin.

Baki daya dai an gudanar zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisa salun alun a jihohin Sokoto Kebbi da Zamfara duk da cewa dai an ba’a fara zabe da wuri ba a wasu rumfunan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG