Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Gawa Ta Bace Masu Gawa Sun Koka

Akwatin Gawa
Akwatin Gawa

Wata 'yar kwarya kwaryar rigima ta faru a garin Mowe, dake cikin jahar Ogun, dake taraiyar Najeriya, game da bacewar gawar wata mata mai suna Ayoka Buhari, 'yar shekaru 55.

A lokacin da iyalan Mrs. Buhari, suka nufi wajen da aka ajiye gawar domin aje a burne sai a mika masu gawar da ba ta Mrs. Buhari, ba wanda yake nufin cewar a mika gawar ga wasu da suma suka kawo ajiyar gawa, a asibitin Gbagada dake Lagos.

Data take jawabi akan bacewar gawar mahaifiyarta Folorunsho Adeoluwa, ta ce zasu nufi kotu domin ajiya suka bada, ta ce da aka fito da akwatin gawar sai ta ce abude ana yin haka sai ta ga cewa ba gawar mahaifiyarta ke ciki ba.

Wani ma'aikacin wajan ajiyar Femi ya ce an yi kuskure ne aka baiwa wani wanda shima ya kawo ajiya gawar mata sa, iyalan sai suka garzaya Matori domin samun mutuni amma sai ya ce masu shi har ya burne gawar, kuma bazai tono gawar ba sai sun nuna mashi hoton gawar da aka basu.

Sun koma sun dauki hoton gawar amma shi mutumi bai dawo ba balle ya ce gawar matar shine ko kuma a'a.

XS
SM
MD
LG