Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun kasar Norwey ta yankewa Breivik hukumcin dauri mafi tsanani


Anders Behring Breivik
Wata kotun kasar Norwe tace mutumin nan da ya amsa laifin kisa Anders Behring Breivik yana da cikakken hankali lokacin da ya kai tagwayen hare hare a watan Yulin da ta gabata ya kashe mutane 77.

Hukumcin da aka yanke yau Jumma’a na nufin cewa, Breivik zai shafe shekaru 21 a gidan yari, yana kuma yiwuwa a kara mashi wa’adin zaman gidan wakafi muddin aka ga yana da hadari. Masu shigar da karar sun so a same shi da tabin hankali domin a tura shi asibitin mahaukata.

Breivik ya amsa laifin kashe-kashen da suka auku sakamakon harin bom da kuma bude wuta da ya yi a wani ginin gwamnati a birnin Oslo da kuma wani sansanin gangamin siyasa na matasa. An yi mashi gwajin tabin hankali har sau biyu, inda wani binciken ya nuna yana da tabin hankali daya kuma yace yana cikin hankalinsa.

Lauyan Breivik yace mutumin da yake karewa ba zai kalubalanci hukumcin ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG