Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotun Soja Dake Maiduguri Ta Yankewa Wasu Jami’an Soja Hudu Hukunci


Kotun Soja Ta Musamman A Garin Maiduguri

Kotun soja a garin Maiduguri ta yanke hukunci ga wasu jami’an soja guda hudu kan wasu laifuffuka da suka aikata daban daban a lokacin da suke gudanar da yaki da mayakan kungiyar Boko Haram.

A cewar shugaban kotun ta musamman Birgediya Janaral Olusegun Adeniyi, wannan kotun zata yi kokarin ganin cewa ta kawo ‘da’a cikin aikin soja musammanma a cikin yanayin da ake na yaki da ‘yan ta’adda.

An dai yanke hukuncin farko ne ga wani jami’in soja dake da shekaru 13 a aikin soja da ake kira Major Mahammed Usman, wanda zai shafe watanni 18 ba tare da matsawa daga mukaminsa na major ba. An dai zarge shi ne da laifin guduwa daga wani kauye da ake kira Tokumbere a karamar hukumar Goza, lokacin da suke yaki da kungiyar Boko Haram, ya koma wani gani na daban ba tare da izinin manyansa ba.

Haka kuma kotun ta yankewa wani mai mukamin Major da ake kira Mohammed Danladi Bello, hukuncin shekaru biyu ba tare da samun karin mukami ba, sakamakon laifin da ake zargin ya aikata, a lokacin da yake kula da tankunan yaki a kauyen Tekumbere, ya kuma janye tankunan zuwa garin Bita ba tare da samun izinin yin hakan daga gurin shugabanninsa ba.

Shima Kaftin Christopher Leche, an yanke masa hukuncin shekaru biyu ba tare da karin mukami ba, bayan samunsa da laifin janye motocin yaki da yayi daga garin na Tekumbere zuwa garin Bita.

A zaman na jiya ne kotun ta sake yankewa wani kurtun soja da ake kira Macdonald Chukwu hukuncin daurin watanni 18 a gidan Yari, sakamakon samun wasu harsashe da akayi a gurinsa har guda 89 a cikin jakarsa a wata tashar mota da ake kira tashar Kano, wanda aka ce ya kamata ya mikasu amma bai yi hakan ba.

Tun da farko dai lauyan dake kare sojojin Barista Sha’aibu Isa, ya nemi afuwa ga mutanen da aka yankewa hukuncin na cewa yakamata kotun ta duba irin halin da mutanen ke ciki, kasancewa mutane ne masu iyalai, kuma sun sadaukar da rayukansu wajen bautawa kasa don haka yakamata kotun ta sassauta hukuncin da zata aiwatar a kansu.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

XS
SM
MD
LG