Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotun Sojin Pakistan Ta Yankewa Wani Dan Indiya Hukumcin Kisa


 Hoton dan Indiya Kulbhushan Jadhav da aka yiwa hukumcn kisa bisa zargin yiwa Indiya leken asiri
Hoton dan Indiya Kulbhushan Jadhav da aka yiwa hukumcn kisa bisa zargin yiwa Indiya leken asiri

Wata kotun ma’aikatar sojin Pakistan ta yanke hukuncin kisa a kan wani dan India da ake masa zargin dan leken asirin kasar Indiya din ne.


Ma’aikatar sojin tacea bara ne aka kama mutumin mai suna Kulbushan Jadhav a lardin Baluchistan.
Indiya ta tabbatar da cewar Jadhav tsohon jami’in sojan ruwan kasarta ne, sai dai ta musanta cewar yana gudanar da ayyukan leken asiri ne. Tace ya yi ritaya daga aikin sojin ne da wuri wuri.

Haka kuma hukumomin na Indiya sun karyata wani faifan bidiyo daaka nuna inda aka ce wai ya amsa laifin yin leken asirin, abinda hukumomin Indiya suka ce ba gaskiya ba ne.

Ya zuwa yanzu dai ba’a tsaida ranar aiwatar da hukuncin kisar ba.

Pakistan ta dade tana zargin Indiya da horarwa tare da bada taimakon kudi ga ‘yan bindiga masu shirya ta’addancin a boye a Baluchistan.

India da Pakistan abokan gaba ne da suka mallaki makaman nukiliya.

Kasashen biyu sun gwabza yake yake sau uku tun bayan lokacin da gwamnatin mulkin mallaka ta Birtaniya ta raba Pakistan da Indiya shekarar 1947 kuma har yanzu suna ci gaba da zaman dar dar da juna.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG