Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotun Tarayyar Najeriya Ta Bada Belin Tsohon Ministan Birnin Tarayya


Alkalin Alkalan Najeriya Justice Onnoghen
Alkalin Alkalan Najeriya Justice Onnoghen

Yau wata kotun birnin tarayyar Najeriya ta bada belin tsohon ministan birnin, Bala Muhammad bisa kudi Naira miliyan dari biyar tare da masu tsaya masa su biyu dake da gidaje a birnin tarayyar kuma har wa yau dayansu ya kasance Sanata

Daya daga cikin lauyoyin dake kare tsohon ministan Bala Muhammad, Chris Uche, SAN, ya bayyana jin dadinsa saboda a cewarsa lallai dimokradiya na aiki a kasar ta Najeriya kan hukumcin da kotun ta yanke.

Tsohon ministan na birnin Abuja ya shiga hannun hukumomi ne biyo bayan kamashin da hukumar dake yaki da cin hanci da zarmiya, wato EFCC tayi akan zargin yin almundahana da dukiyar jama'a da suka kai N864m yayinda yake gwamnati.

Lauyan nasa Chris Uche yace shigar da kara abu ne daban haka kuma tabbatar da hujja akan zargin abu ne daban.

Alkalin ya bada belin tsohon ministan bisa ka'ida ta sa hannu kan Naira miliyan dari biyar da mutane biyu masu tsaya masa cikinsu ko har da mai mukamin Sanata.

Tuhumar ba ita ba ce ta farko da hukumar EFCC take yiwa tsohon ministan ba da wasu jami'ai da dama na tsohuwar gwamnatin Shugaba Jonathan..

Ministan shari'a Abubakar Malami yace akwai wata hukuma ta musamman da zata dinga kula da dukiyoyin da aka kwato daga barayin biro. Dokar kafa hukumar har yanzu tana gaban majalisa.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG