Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kungiya Tana Nema A Tsige Shugaba Goodluck Jonathan


Shugaba Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan

Wata hadakar kungiya tana neman a tsige shugaba Goodluck Jonathan bisa zargin cewa bai yiwa kasa aikin komi ba.

Wadansu kungiyoyi masu zaman kansu sun zaga shiyoyi shida na Najeriya suna tattara sa hanun yan kasa saboda su mika shi ga majalisar dokokin kasar.

Kungiyoyin sunce sun yi wannan yunkurin ne saboda suna nema a tsige Shugaba Goodluck Jonathan akan cewa bai yi wa kasa aikin komai ba tunda aka zabe shi.

Kungiyoyn sun jera laifukan da suke zargin shugaban kasar da aikatawa da suka hada da rashin cika alkawuran da yayi dangane da samar da wutar lantarki, da yaki da cin hanci da rashawa, yawan yajin aiki da ma’aikata ke yi, da kuma kin aiwatar da kasafin kudi.

Sai dai a nasu bangaren, jami’an gwamnati sun ce tunda ake shugabanni a Najeriya ba a taba samun wanda yayi aiki irin Shugaba Goodluck Jonathan ba.

A cikin hirarsu da wakiliyar Sashen Hausa Madina Dauda, kwamred Isa Tijjani, shugaban hadakar kungiyar yayi karin haske dangane da wannan yunkurin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG