Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar "Concerned Nigerians" Ta Ce Shugaba Buhari Ya Dawo Kan Aiki Ko a Tsige Shi


Ginin majalisun tarayyar Najeriya
Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Kungiyar ta yi barazanar zuwa majalisa domin neman ta kafa kwamitin bincike kan lafiyar shugaban.

Wata kungiya mai rajin kare demokuradiyya a Najeriya da ake kira “group of concerned Nigerians”, ta yi kira ga majalisar ministoci data dokokin tarayya su gaggauta kafa komiti da zai tantance lafiyar shugaba Muhammadu Buhari ganin ya kusa cika kwanaki 90 baya kasar.

Shugaba Buhari dai tun a farko farkon watan Mayu ne ya tafi Ingila domin jinya, kodashike a baya bayan nan jami’an kasar wadanda suka ziyarce shi a birnin London, sun ce shugaban ya sami sauki, yanzu umarnin likita ne yake dako.

Shugaban kungiyar ta Concerned Nigerians, Deji Adeyanju, ya gayawa Saleh Shehu Ashaka cewa kungiyar sa zata tafi majalisa ind a zata bukaci majalisar dattijai ta kafa kwamiti kamar yadda tsarin mulki ya tanada domin tantance ko shugaba Buhari yana karfin ci gaba d aaikinsa.

Gameda tasirin wannan mataki ganin shugaban ya mika iko ga mataimakinsa Parfessa Yemi Osinbanjo, Deji yace, shirme ne kawai, har yanzu hadiman Buhari ne suke rike da madafun iko kuma ahalin yanzu komi ya tsaya a cik a kasar.

Kan mataki na gaba da zasu dauka, idan majalisa bata biya musu bukata ba, Deji, yace daga shugaban kasa har zuwa ‘yan majalisa, talakawa suka zabe su, saboda haka tilas ne su yi abunda ‘yan kasa suke so.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG