Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Sabuwa a Danbarwar Siyasar Jihar Taraba


Jihar Taraba

Yanzu haka wata sabuwa ta sake kunno kai a jihar Taraba dake Najeriya game da zargin da akewa mukaddashin gwamnan jihar cewa akwai wata kullaliya a tsakaninsa da yar takarar gwamna ta jam’iyyar adawa ta APC

Tun bayan da kotun koli ta maido da mataimakin Gwamnan jihar Taraba Alhaji Sani Abubakar Danladi, an sake bude wani sabon shafi a danbarwar siyasar jihar cikin watan Nuwambar da ya gabata, game da batun magajin gwamnan jihar wato Dan Baba Suntai dake fama da jinya.

A cikin kwanakin nan ma wasu kafofin yada labarai da Kungiyoyi sun bayyana zargin da ake yi ma mataimakin Gwamnan, wanda yanzu haka shi ke rike da kujerar mukaddashin Gwamnan jihar, cewa akwai zumuncin kud-da-kud tsakaninsa da ‘yar takarar Gwamna ta jam’iyyar APC, wato Sanata Aisha Jummai Alhassan dangane da zaben da ke tafe.

Amma shi kuma Mukaddashin Gwamnan jihar ya musanta zargin da ake yi masa. Haka zalika ita ma ‘yar takarar Gwamna a karkashin jam’iyyar APC, Sanata Aisha Jummai Alhassan ta maida murtani inda tace sharrin ‘yan adawa ne kawai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

XS
SM
MD
LG