Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Shu'umar Wutar Daji Na Cigaba Da Barna A California,


Wani jirgin kashe gobara na shawagi a dajin California
Wani jirgin kashe gobara na shawagi a dajin California

Daruruwan mutane sun bace yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane 31 sanadiyyar wata shu'umar wutar daji a jahar California, inda a yanzu wutar ke cigaba da barna a yankin nan da aka fai noman inabi ciki.

Wutar daji mai matukar ci a sassa daban-daban na shiyyar noman inabi, wadda aka fi sani da "Wine Country" a jahar California, na nemar dunkulewa waje guda, a cewar Shugaban hukumar Kwana-Kwana ta Karamar Hukumar Napa a jiya Jumma'a, a yayin da masu kokarin kashe wutar ke fuskantar matsalar yawaitar busasshiyar iska.

Shugaban Hukumar Kashe Gobarar, Barry Biemann, ya ce hukumarsa na kokarin hada kai da hukumar kashe gobara ta jahar, don su shata kariya a wasu muhimman wurare, saboda a hada wutar yaduwa.

Ya ce 'yan kwana-kwanan sun yi nasarar kashe wutar a wasu wurare jiya Jumma'a, to amma su na iya fuskantar munanan yanayoyi cikin 'yan kwanaki masu zuwa saboda ana kyautata zaton za a fuskanci iska sosai da kuma bushewar yanayi.

Zuwa jiya Jumma'a wutar ta kashe mutane akalla 31 tun daga ranar Lahadi da ta tashi, a yayin da kuma har yanzu ba a ji duriyar fiye da rabin mutane 900 da aka bayar da rahoton bacewarsu tun farko ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG