Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsutsa Ta Lalata Gonaki, Ta Kuma Cutar Da Al'uma A Adamawa Da Taraba.


Wata mace take rike da tsutsar, data yi mata barna a gonarta a kasar Zimbabwe.

Akalla mutum daya ya mutu wasu kuma sun kamu da cututtuka saboda dalilai da ake dangantawa da tsutsar.

Akalla mutum daya ya rasa ransa, wasu uku kuma sun kamu da cuta sakamakon harin da wata tsutsa da ake kira Armyworm da turanci, ta afakawa sassan arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotanni daga jihohin Adamawa da Taraba,arewa maso gabashin Najeriya na cewa, yanzu haka wata tsutsa mai cin hatsi da ta mamaye gonakin mutane a wasu jihohi Najeriya,yanzu haka ta soma cutar da jama’a .

Tsutsar ta yi mummunar barna a gonaki musammam waɗanda shukarsu ba ta yi ƙwari ba, ta fantsama cikin jama’a wanda nan take takan cutar da wanda ta fadawa.

Tsutsar da ake kira armyworms a turance wanda ta mamaye gonaki ta kan fantsama kan shukar manoma musammam amfanin gona irinsu masara da gero da dawa da shinkafa a wasu sassa na Najeriya.

To sai dai kuma baya ga amfanin gona,yanzu haka wannan tsutsa ta fantsama cikin jama’a inda ta kan jawo kuraje da kuma zazzabi ga wanda ta fesawa gubarta,kuma a jihar Taraba tuni ta yi barna a wasu kauyuka da suka hada da Gongon Maliki da kuma Tella,baya ga na Jalingo fadar jihar.

Kamar Taraba,a jihar Adamawa ma ba’a tsira ba,inda tsutsar ta yi barna.Mallam Lawan Danladi na cikin wadanda tsutsar ta fesawa guba,yace jikinsa ya kumbura .

Ko da yake kawo yanzu hukumomin kiwon lafiya basu yi karin haske ba game da wannan batu,to amma wani jami’in kiwon lafiya Muhammad Kabir Jalingo, wanda yayi jinyar wani da ya kamu da cutar tsutsan kira yayi da ake kulawa.

Shima wani malami a tsangayar koyon dabarun aikin gona a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Adamawa ,Abdullahi Musa gargadi yayi ga manoma da a dau mataki.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Facebook Forum

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG