Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Watan Janairun Badi Za'a Kammala Binciken Kisan da Aka Yiwa Sojojin Amurka a Niger


Sojojin Amurka hudu da aka kashe a Jamhuriyar Niger

Ranar hudu ga watan Oktoban wannan shekarar ce aka kashe sojojin Amurka hudu dake taimakawa kasar Niger yaki da ta'addanci a wani kwantan bauna da aka yi masu a yankin dake makwaftaka da kasar Mali

Rundunar sojin Amurka ta ce ba a sa ran kammala cikakken binciken mummunan harin kwantan baunar nan da aka kai watan jiya a Nijar, har sai watan Janairun badi.

Tawagar masu bincike na sojin, wadda ke karkashin Manjo-janar Roger Cloutier, zai ta tafi wasu wurare a Amurka da Afirka da Turai don ta tattaro bayanan da za su taimaka wajen gano abin da ya faru yayin harin na ranar 4 ga watan Oktoba, bisa ga wani bayani na Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon da aka fitar jiya Laraba.

Jami’an tsaro a Pentagon da kuma Ma’aikatan Tsaron Janhuriyar Nijar sun ce mayakan ISIS ne su ka yi kwantan bauna ma sojojinsu a ranar ta 4 ga watan Oktoba, su ka kashe sojojin Amurka 4 da sojojin Nijar su ma 4 da wani dan Nijar mai tafinta.

Sojojin sun kamalla wata ganawa da shugabannin yankin, sun fara tafiya su shiga motocinsu su koma Kenan, sai kwatsam aka kai masu hari, abin da jami’an Amurka su ka gaya ma Muryar Amurka Kenan.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG