Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wilberforce Juta Ya Baiwa Sanata Ali Modu Sharif Shawarar Yayi Murabus


PDP

Kwamitin Ceto PDP a karkashin jagorancin Wilberforce Juta, ya baiwa sabon shugaban Jam’iyyar Ali Modu Sheriff shawar ya yi murabus.

Mista Juta, ya yi wannan furucin ne a wani taron manema labarai a birnin Tarraiyya Abuja. Bayan da wakiliyar Muryar Amurka, Madina Dauda, ta tambayeshi ko menene dalilin taron? Yace, abinda ya faru game da zaben shugaban jam’iyyar PDP ta Najeriya, ba a bi ka’ida ba, domin an bayar da wannan mukami ne a Kudu maso Gabashin Najeriya, inda tsohon shugaba Mu’azu ya fito domin a maye gurbinsa sai gashi an baiwa mutumin da bai kamata ba.

Ko wacce jiha a yankin ta kawo sunayen yan takarar da suke so, banda jihar Taraba wanda suka ce basa bukata, sauran jihohi biyar sun fitar da sunaye. Ana tsammanin cikin sunayen ne za a zabi shugaban jam’iyyar, sai gashi an kawo mutumin da ba a san kowaye ya kawo shi ba an bashi wannan matsayi.

Ganin cewar Sanata Ali Modu Sharif bai dade a cikin jam’iyyar ba, hakan ne yasa wasu jigogin jam’iyyar ke cewa basu san yadda akayi ya samu wannan kujera ba. Mista Juta dai yace tunda yake kowa ya sani ba a amince da abinda ya faru ba, don nema suka yi kira ga duk kwamitocin jam’iyyar da a zauna domin samar da masalaha.

Saurari hirar Madina Dauda da Wilberforce Juta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:09 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG