Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dawo Da Wutar Lantarki A Wasu Yankunan Arewacin Najeriya


Ma'aikata na gyara a wasu turakun wutar lantarki a Najeriya (Hoto: X/TCN)
Ma'aikata na gyara a wasu turakun wutar lantarki a Najeriya (Hoto: X/TCN)

“Yayin da ake ci gaba da gyare-gyaren, tawagar injiniyoyinmu na shirin fara aiki akan layin 330KkV na biyu.” In ji Mbah.

Kamfanin TCN mai raba wutar lantarki a Najeriya ya ce an gyara layin wutar Ugwuaji-Apir mai karfin 330kV da yammacin Laraba bayan da injiniyoyi suka kammala ayyukansu.

Wata sanarwa da kamfanin ya fitar dauke da sa hannun kakakinsa Ndidi Mbah, ta ce yanzu “lafia, Makurdi, Jos, Kaduna, Kano, Bauchi da Gombe na da wuta.”

An doshi kusan makonni biyu babu wutar lantarki a daukacin arewacin Najeriya sanadiyyar barnata kayayyakin wutar lantarki da ‘yan fashin daji suka yi akan layin na Ugwuaja-Apir.

“Yayin da ake ci gaba da gyare-gyaren, tawagar injiniyoyinmu na shirin fara aiki akan layin 330Kv na biyu.” In ji Mbah.

Rahotanni sun nuna cewa katsewar wutar lantarki ta haifar da dumbin asara ga masana’antu, ‘yan kasuwa da kananan ma’aikatu cikin kwanakin da aka kwashe babu wutar.

Kungiyar Masana’antu ta Najeriya a Kano ta ce mambobinta sun tafka asarar biliyoyin naira cikin takin lokacin da aka kwashe babu lantarki a sassan arewacin Najeriyar.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG