Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata Hausawa Da Fulani Su Yi Ma Kawunansu Fada Game Da Polio In Ji Shaihin Malami


Sheikh Dr. Ahmad Gumi yace Musulunci bai hana karbar allurar rigakafi ba, kuma duk manyan kasashen Musulmin duniya sun rungumi rigakafin Polio in ban da Hausawa da Fulanin arewacin Najeriya

Sanannen shaihin malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi, yace ya kamata Hausawa da Fulani dake arewacin Najeriya su yi ma kawunansu fada a game da yadda suke nuna kyamar maganin rigakafin cutar shan inna ta Polio.

Sheikh Gumi yace a kowace kusurwa ta duniya, Musulmi da kasashen Musulmi su na karbar wannan rigakafi hannu bibbiyu domin su raba 'ya'yansu da cutar mai gurgunta wadda ta kama, a yayin da Hausawa da Fulani kadai a Najeriya suke nuna turjiya.

Yace ko a cikin Najeriya, yankunan kudancin kasar su na karbar wannan rigakafi hannu bibbiyu, kuma a arewacin Najeriya din ma, sauran kabilu su na karba, sai Hausawa da Fulanin kadai ke nuna kyamar wannan maganin mai matukar amfani.

Yace Musulunci bai haramta maganin rigakafi ba, kuma akasarin manyan malaman addinin Musulunci a fadin duniya sun hadu sun yi ittifaki da cewa karbar maganin rigakafin cutar shan inna ta Polio yana da amfani kuma ya kamata a yi shi.

Yace dukkan manyan kasashen Musulmin duniya kamar su Saudi Arabiya, Masar, Indonesiya, da kasashen arewacin Afirka na Musulmi duk su na karbar wannan maganin.

Ya shawarci Hausawa da Fulani da su rungumi wannan maganin.
Musulunci Bai ce Kada a Karbi Rigakafin Polio ba - Sheikh Dr. Ahmad Gumi - 1:28
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG