Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Kano na Fafutukar Wayar da Kan Jama’arta Game da Rigakafin Polio


Masu fama da cutar shan inna
Masu fama da cutar shan inna

Shugabar masu lalurar shan inna ta Jihar Kano, Amina Abdullahi Getso, ta ce wayar da kan na da kyau, amma ana bukatar gyara kan yadda masu unguwanni ke ba iyalansu aikin rigakafin.

Jihar Kano dake yankin arewacin Najeriya ta dukufa wajen wayar da kan jama’a da su rungumi rigakafin cuce-cucen da ake bayarwa, musamman na cutar shan inna ko Polio, bisa kwakkwarar hujjar cewa yin hakan ne kawai zai iya tabbatar da kare lafiyar yara ‘yan kasa da shekara 5.

Wannan yana kunshe a cikin bayanin da jami’an kiwon lafiyar jihar suka gabatar a zauren taron da Muryar Amurka da Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Amurka, CDC, suka shirya a Kano domin nazarin hanyoyin cimma gurin kawar da cutar Polio.

Daya daga cikin wadanda suka yi bayanai a zauren taron it ace shugabar kungiyar masu lalurar shan inna ta Jihar Kano, Malama Amina Abdullahi Getso, wadda ta yi bayanin irin yadda cutar shan inna ta ke yin illa a jikin dan Adam, da irin takurarwar da ta ke yi wajen sauya rayuwa baki dayanta, ta wanda ya kamu da cutar da kuma ta iyayensa da ‘yan’uwansa.

Sannan ta koka a kan yadda masu unguwanni suke sanya sunayen iyalansu da ‘yan’uwansu a zaman wadanda zasu yi aikin bayarda maganin rigakafin, su kuma sai suje su samo wasu mutanen sun a biyansu domin su yi.

Ta ce a irin wannan yanayin, ba a gudanar da aikin yadda ya kamata domin wadanda ake bas u aikin bas u iya ba, su kuma sun a samo wadanda bas u da kwarin guiwar yin aikin tun da ba wani abin kirki zasu samu ba.

Ta bukaci fgwamnati da hukumomin kiwon lafiya da dukkan masu hannu a wannan gangami na yaki da cutar Polio da su nazarci wannan batu domin a iya cimma bukatar bayar da maganin rigakafin yadda ya kamata.

Amina Abdullahi Getso, Shugabar Masu Fama da Polio a Kano - 3:32
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG